JAMB 2026 REGISTRATION EXPECTED OPEN: ON FRIDAY JANUARY 31/01/2026 CIKAKKEN JAGORA GA DALIBAN NIGERIA

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu a Najeriya, wato Joint Admissions and Matriculation Board (JAMB), Ana hasashen zata bude shirin rajistar JAMB 2026 domin bai wa dalibai damar shiga jami’o’i, polytechnic da colleges of education a fadin kasar nan. Wannan labari zai yi bayani dalla-dalla kan duk abin da dalibi ke bukata ya sani game da JAMB 2026, tun daga rajista, sharudda, matakai, kudade har zuwa shawarwari masu muhimmanci.
Menene JAMB?
JAMB hukuma ce ta gwamnatin tarayya da aka kafa domin tsara jarabawar shiga manyan makarantu a Najeriya. Ita ce ke shirya UTME (Unified Tertiary Matriculation Examination), wacce ke zama sharadi na farko kafin dalibi ya samu gurbin karatu a jami’a ko sauran manyan makarantu baki daya.
JAMB 2026 Registration Expected Open On Friday 31/01/2026 – Me hakan ke nufi?
Lokacin da aka ce “JAMB 2026 Registration Open”, hakan na nufin cewa Ana hasashen Friday 31/2026 hukumar JAMB zata fara karɓar rajistar dalibai da ke son rubuta jarabawar UTME ta shekarar 2026. Wannan dama ce ga duk daliban da suka kammala ko ke dab da kammala karatun sakandare su fara shirin cimma burinsu na karatun gaba.
Wa Zai Iya Yin Rajistar JAMB 2026?
Ba kowane mutum ba ne zai iya yin rajistar JAMB. Akwai wasu sharudda da dole ne dalibi ya cika su:
1.Dalibi ya kasance yana da sha’awar shiga jami’a, polytechnic ko college of education.
2.Dole ne ya kammala ko yana dab da kammala SSCE (WAEC, NECO ko NABTEB).
3.Dole ne ya kasance yana da shekaru mafi ƙanƙanta da dokar ilimi ta amince da su.
4.Ya kasance yana da National Identification Number (NIN).

Muhimmancin NIN A JAMB 2026
Daya daga cikin manyan abubuwan da ba za a iya kaucewa ba a JAMB 2026 shi ne NIN. Ba tare da NIN ba, dalibi ba zai iya samun profile code ko kammala rajista ba. Wannan na nufin cewa duk dalibi ya kamata ya tabbatar yana da NIN tun kafin ya fara shirin rajista.
Matakan Yin Rajistar JAMB 2026
Ga yadda ake yin rajistar JAMB 2026 a sauƙaƙe:
(1). Samun Profile Code
Dalibi zai tura NIN dinsa ta SMS zuwa lambar da JAMB ta tanada domin samun profile code.
(2). Siyan JAMB ePIN
Bayan samun profile code, dalibi zai sayi JAMB ePIN ta:
.Bankuna
.POS
.Online platforms
(3).Zuwa Cibiyar CBT
Dole ne dalibi ya je cibiyar CBT da JAMB ta amince da ita domin:
.Cike bayanai
.Daukar hoton fasfo
.Yin fingerprint
.Zaben makarantu da courses
(4).Buga Slip
Bayan kammala rajista, dalibi zai karɓi slip wanda ke dauke da cikakkun bayanansa.
Farashin Rajistar JAMB 2026
Kudin rajistar JAMB yawanci ya kunshi:
.Kudin rajista
.Littafin karatu
.Kudin CBT centre
Ko da yake farashi na iya bambanta kadan daga wuri zuwa wuri, ana shawartar dalibai su rika yin rajista a wuraren da JAMB ta amince da su kawai domin gujewa damfara.
Zaben Makaranta da Course
A lokacin rajista, dalibi zai zabi:
.Makaranta ta farko (First Choice)
.Makaranta ta biyu (Second Choice)
Haka kuma, Mutum zai zabi course da yake da sha’awaryi, kamar haka:
.Medicine
.Law
.Engineering
.Education
.Mass Communication
.Computer Science
Ana shawartar dalibi ya zabi course da:
.Yayi daidai da sakamakonsa
.Yana da sha’awa a kai
.Wannan zai bashi Yana da damar samun admission
JAMB UTME 2026 – Yadda Jarabawar Ke Gudana
Jarabawar JAMB UTME 2026 za ta kasance Computer Based Test (CBT). Dalibi zai rubuta jarabawa a cibiyar da aka tanadar masu, a ranar da aka ayyana.
Jarabawar ta kunshi:
.English Language (tilas)
.Sauran darussa 3 bisa ga course
Abubuwan Da Dalibi Ya Kamata ya Kula Da Su Kafin Jarabawa kamar haka:
(1).Ya fara karatu da wuri
(2).Ya sayi JAMB syllabus
(3).Ya yi amfani da past questions
(4).Ya yi mock test idan akwai
(5).Ya guji yaudara da jita-jita
Amfanin Yin JAMB Mock Exam
Mock exam na taimaka wa dalibi:
.Sanin yadda CBT ke aiki
.Rage fargaba
.Gwada ilimin da yake da shi
Ko da yake ba dole ba ne, amma yana da matuƙar amfani ga sabbin dalibai.
Bayan Rubuta JAMB 2026 – Me Zai Biyo Baya?
Bayan jarabawa:
1.Dalibi zai duba sakamakon JAMB
2.Makarantu za su fara post-UTME
3.Za a fitar da admission list
4.Dalibi zai duba CAPS
5.Idan an samu admission, sai a fara shirin karatu
Muhimmancin JAMB CAPS
JAMB CAPS (Central Admission Processing System) shi ne tsarin da ake:
.Karɓa ko ƙin admission
.Bibiyar matsayin admission
.Tabbatar da sahihancin admission
Duk dalibi dole ne ya rika duba CAPS akai-akai.
Gargadi Ga Dalibai
.Kada a bari a yaudare ku
.Kada a bi mutane masu ikirarin “sai na saka ka”
.Kada a yi rajista a wurin da ba a amince da shi ba
.Kada a bada bayanai ga wanda ba a yarda da shi ba
Kammalawa
Bude rajistar JAMB 2026 wata babbar dama ce ga dubban daliban Najeriya da ke burin samun ilimi mai zurfi. Yin rajista da wuri, bin ka’idoji, da kuma yin shiri mai kyau zai taimaka matuka wajen samun nasara. Idan dalibi ya bi duk matakan da suka dace, babu shakka zai kasance cikin wadanda za su cimma burinsu na shiga manyan makarantu gaba da sakandare.








